Suwanene mu?
Manufofin mu
Mu rukunin masu bin Allah ne, waɗanda suka sami hanyar zuwa Bege ta wurin bincike, biyayya, da yaɗa gaskiyar Maganar Allah.
Manufarmu itace taimakon mutane domin samun gaskiyar Maganar Allah.
Samun Ilimi na Musamman
Bayan mun gwada dukan abubuwan da duniya ta tanada domin biyan muradin zuciyarmu, mun gano cewa waɗannan abubuwan wato; ƙudi, iko, nasara, sanayya, da sauransu duk aikin banza ne.
Muna tabbatar muku da dukan zuciyarmu cewa za ku sami amsoshin tambayoyinku na fama a rayuwa. Rayuwarku tana da manufa, ku ma za ku iya binciko waɗannan gaskiyar tare da wasu da suke neman ma’ana da manufar rayuwa.
Sakon Allah
Allah ya aiko Isa Almasihu cikin duniya tare da sako ga dukan mutanen duniya. Sakon shi ne:
- “Na zo domin in ba ku Rai a yalwace."
-
“Ni ne hanya, ni ne gaskiya, ni ne kuma rai. Ba mai zuwa wurin Uba, sai ta wurina.”